6 Afirilu 2021 - 13:23
Shugaban Kasar Rasha Ya Rattaba Hannu Kan Doka Wacce Ta Bashi Damar Sake Tsayawa Takarar Shugabacin Kasar Har Sau Biyu Nan Gaba

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu a kan doka wacce ta bashi damar tsayawa takarar shugabancin kasar hau sau biyu nan gaba idan ya zabi yin hakan.Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa shugaban, a halin yanzu yana shugabancin kasar karo na hudu ne, wanda zai kare a shekara ta 2024.

ABNA24 : Dokar wacce aka kafa ta bayan zaben raba gardawa wanda aka gudanar a shekarar da ta gabata, ta bawa shugaban damar kara wa’adi biyu na shugabancin kasar na kuma shekaru shida-shida wanda zai bashi damar rike kujerar shugabncin kasar har zuwa shekara 2034.

Da farko Putin ya zama shugaban kasar Rasha ne bayan da Boris Yeltsin yay i murabus a shekara ta 2000.

Bayan wa’adi biyu, Putin ya zama firai minister a shekara ta 2008. Sannan aka sake zabens a matsayin shugaban kasa a shekara ta 2012.

342/